Jiya da safe, ina tafiya a wani Keke Napep, sai wata ƙaramar yarinya ta tsayar damu, ta kalli driver tace:
“Mai Keke, ina kwana?”
Yace: “Lafiya ƙalau, yakike?”
Tace: “Alhamdulillah.”
Yace: “Ina za ki je?”
Tace: “School gate. Za ka kai ni? Nawa ne kudin?”
Yace mata: “₦300.”
Sai tayi shiru kamar ba za ta ce komai ba. Sai na ga ta sunkuyar da kanta ƙasa, idanunta sun yi ja kamar za ta yi kuka. Sai tace:
“Mai Keke Napep, ina da naira ɗari. Za ka ɗauke ni?”
Saiyace: “A’a, ba zan ɗauke ki ba gaskiya, sai kin bani ₦300.”
Sai tace: “To shikenan, ka tafi kawai. Idan ma ka ɗauke ni, ban san waye zai dawo da ni ba. Dama wannan naira ɗarin ita kaɗai ce mamarmu ta bani.”
Kuma saida na ce mata: “Ba za a ɗaukeni ba.”
Tace: “In yi haƙuri in tafi, ba ta da kuɗi.”
“wai nayi tawakkali ga Allah. Mutanen kirki ba su ƙarewa. Akwai masoya Manzon Allah. Idan wani bai ɗauke ni ba, wani zai ɗauke ni.”
Sai driver yace: “To shikenan, ki riƙe ɗarinki, na bar miki hawo mu tafi.”
Sai da muka tafi, saina kalleta nace mata:
“Babanki yana nan ko ya rasu?”
Sai tace: “Babanta sojane. Idan ya tafi, yana ɗaukar lokaci mai tsawo bai dawo ba.”
Saina ƙara tambayarta:
“Waye yake baki kuɗin hawa mashin kullum idan za ki zo school?”
Tace: “Babantane yake tura musu kuɗi duk ƙarshen wata. Idan suka sayi kayan abinci, sai a rage kuɗin da ake bata domin zuwa school.”
Again saina kara tambayarta:
“To yanzu kuɗin sun ƙare ne, ko ya aka yi?”
Sai tace:
“Ai mamartace tayi rashin lafiya, aka kaita asibiti. Aka yi mata ƙarin ruwa, da ƙarin jini. Aka kira babansu aka sanar da shi, yace wallahi ba shi da kuɗi saboda yanzu wata yayi nisa.”
“Sai dai suka sayar da kayan abincin da suka siya, suka haɗa da kuɗin Keke Napep da ake bata domin zuwa school, suka biya kuɗin maganiYanzu ma Koko Tasha tataho school.”
Ni dai inata yimata tambaya cikin tausayi kamar nayi hawaye🥲 sai nace:
“Kinayin Islamiyya?”
Tace: “Eh. A Kano tana zuwa Islamiyya, amma tun da suka dawo Abuja ba a sanya ta ba. Sai dai kullum mamarta tana koya mata karatun Al-Qur’ani cikin gida.”
Duk tambayar da nayi mata, sai in ji ta bada amsa daidai da tambayar. Ni kaina sai da nayi mamaki ganin ƙaramar yarinya kamar wannan, amma tana da ilmi sosai da hankali.
Har muka zo bakin gate ɗin makarantar, Inada 1500 a aljihuna Zambia 500 kufin keke napep sai na dauko 1000 zan bata,
Bayan tasauka za ta tafi, sai driver yace naji duk abunda kuke magana akai saboda haka kabar dubu ɗayanka 1k dinka,
mutumin ya kirata ta dawo.
Ya zaro ₦7,000 ya bata yace:
“Ki ɓoye su da kyau kada su ɓace. Idan kin koma gida, ki ba mamanki, kice ta siya muku abinci na ₦5,000, A'ajiye miki ₦2,000, A riƙa baki kuɗin Keke Napep daga nan kafin a yi wa babanku albashi. Idan kin je, kicewa mamamki masoyin Manzon Allah ne ya baku.”
Sannan ya zaro ₦500 ya bata yace:
“Ki riƙe wannan, ki haɗa da ɗarin da ke gurinki. Ki yi breakfast da ₦300, ki ajiye ₦300 ki biya Keke Napep idan an tashi ki koma gida,
sai bayan yarinyar Tatafi nakalli mutumin nace Amma bawan Allah kaima sojane kodai wani ma'aikacin gomnati?
yakalleni yayi dariya yace a'ah babu ko daya wllh shi kayan Miya yake siyarwa yanzu haka ma kasuwa yanufa,
duk abunda yayimata yayimatane saboda Allah da arzikin Manzon Allah kamar yarda mahaifiyarta tanunamata,
saikuma ganin yarinyar tanada kokari sosai Gameda addinin musulunchi shiyasa yabata kudin.
____----------________----------__________-----------::: Allah ubangiji kakaramana soyayyar Annabi Mohammed s.a.w
true life story:::