AJIYE MAGANAR FEMINIST, MATA DAYAWA YANZU BA NA AURE BANE....
Ba duk mace ce aka halicce ta domin aure ba, ka maimaita wannan a hankali...
Wasu matan ba su dace da rayuwar aure ba; abin da suke nema kawai shi ne nishaɗi da jin daɗin ɗan lokaci. Ba za su iya ɗaukar nauyin alƙawari ko gina rayuwa mai ɗorewa da kai ba. Don haka abu mafi muhimmanci shi ne ka iya bambance tsakanin macen da ta shirya aure da wadda ba ta shirya hakan ba.
Wasu matan na samun nishadi ne kawai na wucin gadi, wasu kuma irin matan da za ka iya gina rayuwa da su ne. Idan ka rikita waɗannan biyun, kai da kanka zakayi kuka.
Ka daina ƙoƙarin mayar da abin da ya saba zama na kowa, abin da ya saba zama a titi ya zama naka na sirri kai kadai. Gidan haya ba zai taɓa zama gidan zama na har abada ba. Tituna suna da nasu, kuma sau da yawa abin da ya saba da titi ya kan koma inda ya fito... Anan ba sai na bada misali.
Idan ka shigo da rayuwar titi cikin rayuwarka ta sirri, kada ka yi mamaki kuma don ta ƙi barin halayen titin a waje. Za ta shiga cikin kwanciyar hankalinka, gidanka, har ma da makomarka. Kuma mafi muni? Wata rana za ka gane cewa kai ne ka jawo wa kanka duk hakan.
Wasu matan ba sa daina wannan salon rayuwar na titi, kawai suna ɗan dakatawa ne. Suna yin shiru na ɗan lokaci domin su sake gina amana, su huta, sannan su koma wasan da cikakken ƙarfi.
Shiru na ɗan lokaci ba ya nufin mutum ya canza. Ɗan karkacewa daga hanya ba ya zama tuba da gyara kai tsaye. Idan mutum bai canza tunaninsa da halayensa ba, tsohuwar rayuwa na iya sake jan sa ya koma.
Feminist sunyi expired, sun riga sun zama tsumma da aikinsa kawai goge datti na ɗan lokaci, kuma duk kakar wankin da zakayi masa? Za a gane tsumma ne.
Auren macen da ba ta dace da kai ba tamkar ka shuka bishiyar mangoro ne a kasuwa, sannan ka yi tsammanin babu wanda zai hau ya debi yayansa. Wannan ba zai yiwu ba.
Za ka kwashe rayuwarka kana gadin ta, kana korar masu shigowa, kana ƙoƙarin kare abin da kake ganin naka ne, har sai ka fahimci cewa babban kuskuren tun farko naka ne.
Ka ga alamomin, amma ka yi biris da su. Ka yi ƙoƙarin sake rubuta tarihinta. Ka shawo kan kanka cewa za ta canja.
Amma tarihi ba ya yin ƙarya. Gaskiya kuwa ko an binne ta na ɗan lokaci, wata rana sai ta sake bayyana.
Idan abin da kake nema kawai shi ne nishaɗi, to ka more lokacinka. Amma kada ka taɓa rikita jin daɗin ɗan lokaci da abin da zai dawwama.
Matar da ta dace da aure tana ɗaukar kanta da mutunci, tana girmama mijinta, kuma tana daraja amana. Ba ta mayar da yawo akan titi rashin hankali ya zama salon rayuwarta.
Mata zasu rusheka idan baka fahimcesu ba.