FASFO DIN SHAYKH IBRAHIMA NIASS (RA) ๐
Idan kana so ka ga yadda rayuwar da aka sadaukar ga Allah yake, to kawai ka kalli wadannan fasfofi masu kyau. Shaykh Ibrahima Niass (RA) malami ne haziki wanda ya ketare iyakoki da tekuna da manufa guda daya tak: Don ziyartar Annabi (๏ทบ) da kuma yada sakon Musulunci.
Ya ziyarci kasashe daban-daban da yawa, ciki har da: Ghana, Mali, Najeriya, Gambia, Masar, Sudan, Morocco, Mauritaniya, Guinea-Conakry, Pakistan, London, Saudi Arabia, Paris da dai sauransu.
A cikin littafinsa na wakoki (Diwan), Shehu ya yi nazari a kan dogayen tafiye-tafiyen da ya yi kuma ya rubuta:
ุนูููููุชู ุงููุจูุญูุงุฑู ุงูุฒููุงุฎูุฑูุงุชู ููุฅููููููููู
ุนูููููุชู ุงููููุฑูู ููุงููู
ูุฏููู ุจููููู ุงููุฌูุจูุงูุงู
"Na haye manyan tekuna masu tarin yawa, na ketare kauyuka, birane, har ma da duwatsu. Burina daya tilo shi ne neman yardar Mahalicci na ta hanyar hidima ga addininsa."
Shehu bai yi tafiye-tafiye don neman suna ko hutawa ba. Ya yi ne kawai don yardar Allah da kuma hidima ga addininsa. Alhamdulillah! Allah ya ya albarkarci rayuwarmu Albarkar rayuwar Shehu Ibrahima Niass (RA)
Ina Son SHEHU Rta, Haqiiiqanin Soyayya.
Allah ya tabbatar damu a hakan๐ค๐๐ฟ