ABINDA KE FARUWA A WEB3!
1. Bitcoin ya haura $85K bayan masu sayarwa sun janye orders, yayin da sell na gaba yake kusa da $87K, a cewar Glassnode.
2. Amurka ta ƙara jobs 29,000 a Satumba, ƙasa da 90,000 da ake tsammani. Unemployment ya tashi zuwa 4.2%.
3. Anthropic tayi gargadin cewa matsayin gwamnati game da kamfanin na iya shafar alaƙarsa da kwastomomi, kamar yadda IPO prospectus ya nuna.
4. A watan Afrilu, kashi 2% kawai na gidajen Amurka ke biyan kuɗin AI services, yayin da amfani da AI a kamfanoni ma har yanzu bai yi yawa ba, a cewar a16z.
5. Ana sa ran Trump zai naɗa tsohon Shugaban SEC, Jay Clayton, a matsayin White House AI czar, a cewar CNN.
6. Strategy ta zarce Saudi National Bank, inda ta zama kamfani na 385 mafi girma a duniya, a cewar BTC Treasuries.
7. Asara ta fannin tsaron crypto ta kai $1.26B a Q3, sama da 53.9% daga Q2. Bitget hack na $387.5M ya kai kusan 31% na asarar.
8. Core Lightning ta buƙaci masu amfani da v26.06.7 ko old version su yi update nan take saboda rahotannin hare-hare kan nodes da ba'a sabunta ba.
9. Stand With Crypto EU tace sama da Turawa 50,000 sun rubuta wa European Commission suna neman a ba da damar stablecoin rewards yayin bitar MiCA.
10. Sabuwar dokar Alabama kan crypto ATM fraud ta fara aiki. Masu gudanar da ATM za su mayar da kuɗin sabbin kwastomomin da aka yaudara gaba ɗaya, tare da fees.
11. Official Trump memecoin team ta sanar da dinner da Trump a ranar 22 ga Nuwamba, inda top 185 holders za su samu damar halarta.
Wane labari ne yafi jan hankalin ka?