💭 𝗪𝗮𝗻𝗶 𝗔𝗯𝘂 𝗠𝗮𝗶 𝗠𝘂𝗵𝗶𝗺𝗺𝗮𝗻𝗰𝗶 𝗗𝗮 𝗠𝘂𝗸𝗮 𝗙𝗮𝗵𝗶𝗺𝘁𝗮....
Mutane da yawa suna ganin babban abin da ke hana matasa yin aure shi ne rashin kuɗi.
Amma da muka saurari mutane, muka kalli rayuwa, muka kuma yi tunani sosai...
Mun fahimci cewa ba kuɗi kaɗai ba ne matsalar.
Sau da yawa, rashin tsari ne.
Akwai wanda yake samun kuɗi, amma bai san yadda zai tsara su ba.
Akwai wanda yake da burin yin aure, amma bai san daga ina zai fara ba.
Akwai wanda yake jira sai ranar da za a fara shirye-shiryen aure, alhali shiri ya kamata ya fara tun kafin wannan lokaci.
Shirye-shiryen aure ba wai tara kuɗi kawai ba ne.
✅ Shiri ne.
✅ Haƙuri ne.
✅ Tsara abubuwan da suka fi muhimmanci ne.
✅ Ɗaukar ƙananan matakai domin samun kwanciyar hankali gobe ne.
Muna da yaƙinin cewa idan matasa suka fara shirya aurensu tun da wuri, ko da da ƙananan kuɗi ne, za su rage damuwa, su ƙara samun kwarin gwiwa, kuma su kusanci cika burinkansu.
Wannan shi ne dalilin da ya sa ake gina 𝙏𝙬𝙚𝙯𝙤𝙣.
Ba domin ya maye gurbin ƙoƙarinka ba...
Sai domin ya ba ka tsari da zai taimaka maka ka cimma burinka cikin sauƙi.
💙 A ganinku, mene ne abu na farko da ya kamata mutum ya fara tanada idan yana shirin aure?
Muna son karanta ra'ayinku a comments. 👇
#Twezon #ShiryeShiryenAure #Aure #Tsari #Matasa #Hausa