Mr. Peter Obi ya kara bani kwarin gwiwar ba shi kuri'a ta a 2027 bayan hirarsa da BBC Hausa...
Madina tace: “Ka yi wa ’yan Najeriya alkawarin yin wa’adin shekara hudu a kan kujerar shugaban kasa. Shin ba za ka kamu da son mulki ba bayan wa’adin?”
Mr. Peter Obi yace: “Ba zan kara kwana daya bayan shekaru hudu ba. Ina kwadayin yin aiki ne, ba ina kwadayin yin mulki ba.”
A kan matsalar tsaro, Obi yace ba zai zauna a Abuja yana ta bada umarni ba, zai dinga zuwa wuraren domin gani da idanunsa. Abin da ake bukata shi ne shugaban kasa ya saka a ransa cewa matsalar za ta zo karshe. Masu aikata laifi nan an san su, suna cikin daji, saboda haka za mu nemo su.
Madina tace: “Amma dai zan ganka a Jejina, domin nima zan dinga zuwa aiki.”
Mr. Peter Obi yace: “Ai Madina, idan na zama shugaban Najeriya, ba zan bar kasar nan ba, ba zan je hutu ko na kwana daya ba a cikin shekaru hudun. Zan yi tafiya ne kawai saboda wasu dalilai, amma ba don hutu ba.”
“A cikin shekaru hudun, zan yi hutuna a nan Najeriya, a Zamfara, ko Sokoto, ko Jos. Zan je wuraren da aka fi fama da matsala. Ina so in yi amfani da damar hakan wajen tattaunawa da jama’a.”
A bangaren tallafin mai, Obi yace cin hanci da rashawa su ne babbar matsalar, kuma zai yi maganin cin hanci da rashawar da ake yi a bangaren tallafin mai. Cin hanci ne ya tsala bangaren tallafin mai. Abin da zan yi shi ne kawar da cin hanci sannan a ci gaba da bada tallafin.
“Idan ba ka sata, matarka da ’ya’yanka ba sa sata, za a rage wannan matsalar da kaso 50 cikin 100.”
Madina tace: “Buhari ya taba cewa zai yi maganin cin hanci da rashawa, amma hakan bai yiwu ba.”
Obi yace: “Tsaya, tsaya Madina. Bambanci na da Buhari shi ne, shi bai kasance mai cikakken iko ba. Ni kuma zan kasance mai cikakken iko a gwamnati.”
Madina tace: “Za ka janye idan aka samu dan takara guda daya ka goya masa baya?”
Obi yace: “A bar mutane su zabi wanda suke so.”
Madina tace: “Ba za ka janye ba kenan?”
Yace: “No, no... Ki yi tunani. Idan mutum daya ya samu kuri’u miliyan 20 fa?”
Idan ka ci zabe a 2027, za ka sake yin takara?
Obi yace: “Lokaci na kara tsufa, amma kila in yi idan ta kama. Amma ina son Najeriya ta zama kasa da yaran da aka haifa bayan samun ’yancin kai za su yi mulki.”
Me yasa baka zabi mataimaki matashi ba, duk da ka ce kana son matasa su mulki Najeriya?
Obi yace: “A’a, a’a. Kwankwaso idan aka kwatanta shi da sauran ’yan takarar Najeriya, matashi ne. Aikin yana bukatar wanda ya goge. Kwankwaso yana da gogewa a bangaren siyasa.”
Nigeria will be OK 👍
Peter Obi ya cancanta. 🇳🇬
Abdallah karwai ✍️
6/9/2026
Fatima Raka